Ibrahim Danko - Sarkin Kida Da Waka

Mawaki Ibrahim Danko

A yau Dandali ya samu zantawa da wani mawaki Ibrahim Danko, wanda aka fi sani da mai kida mai waka , ya kuma bayyana yadda ya tsince kansa a harka waka.

Yace “wani bawan Allah ne mai busa Sarewa, idan an harka guje guje da tsale tsale a makarantar mu yana busa Sarewa wasu kuma na yi masa kida muna kuma yi wake toh, daga nan ne sha’awar ta samo assali, sai na koyi busa Sarewa, batare da sanin cewa zata kasance hanyar cin abinci ba.”

A Jos, ina shago wajen aski, abokai na masu zuwa suna ji ina busa Sarewa, a wannan lokacin sai suka ce suna da wani Fim, saboda haka suna bukatan in busa masu Sarewa, bayan da aka kamala wannan Fim din sai suka wajen da ake tace Fina Finai, sai shi mai wannan kamfanin yayi tabaya cewa ina suka samu Sarewa, ta Fulani, sosai sai suka ce ai abokinsu a Jos, sai yace babu wani Bahaushe, da zai iya busa wannan Zarewa a Jos, sai yace toh a kawo ni.

Bayan da aka kai ni sai aka sani a Studio, aka ce inyi busa a tabbatar cewa ni din ne nako yi su kala kala, toh yanzu ga kayan zamani, ana so in zama mutune na farko wanda za’a koyawa wannan abun a arewacin Najeriya, kuma za’a biya ni albashi, tunda na taso dama ina son waka sai na fara koya, ina kan koya sai aka kawo makada kamar mutane biyar wanda kowane bangare da inda ya kware toh gaskiya ni na hadasu gaba daya kuma na kara da kida irin na Sudan.