Microsoft Ya Biya Wata Mata Diyya

Tambarin Microsoft

Kamfanin Microsoft ya biya wata mata diyyar kudi masu dimbin yawa, bayan da manhajar kamfanin ta Window 10 tayi kokarin sauke kanta cikin kwamfutar matar, kuma aka sami akasi wajen saukar manhajar.

Microsoft ya biya Teri Goldstein, wadda ke zaune a jihar California dake Amurka Dala Dubu Goma kwatankwacin Naira Miliyan 2.8, duk a dalilin kwamfutar matar ta lalace bayan da manhajar Window 10 tayi kokarin saka kanta cikin na’urar ta, wanda hakan yayi sanadiyar daukar kwanaki kafin ta sami kan kwamfutarta.

A cewar Goldstein, ita bata taba jin labarin manhajar Window 10 ba, kuma babu wanda ya taba tambayarta ko tana son a saka mata manhajar cikin kwamfutata ba.

An dai zargi kamfanin Microsoft da yiwa masu amfani da kayansa wayo wajen sakasu sabunta manhajarsu zuwa Window 10, ta hanyar yin amfani da alamar cire tallar da suke yiwa mutane wato da zarar mutum ya kokarin cire tallar sai kawai manhajar da fara sauka a na’urar mutane.

Your browser doesn’t support HTML5

Microsoft Ya Biya Wata Mata Diyya - 1'01"