Matukar Matashi Yayi Karatu, Zai Cimma Burinsa Na Rayuwa

Aisha Muhammad Sabo, matashiya da ta karanci kwas din Turanci da harkar koyarwa. Duk da cewar ba abin da ta so ta karantawa ba kenan. Mahaifinta ya so ta karanci harkar Lauya, ita kuma burinta shine ta karanci fannin aikin Jarida.

Kasancewar ba abin da ta so ta karantawa ba ne, hakan ce ta sa ta dan yi wasa a lokacin da ta fara karatunta, sai daga baya ne ta nutsu ta mai da hankalinta wajen baiwa karatun na ta muhimmanci.

Ta ce, daga cikin dan kalubalen da ta fuskanta bayan ga yajin aiki da ake yawan samu na makarantun jami’a, sai yar matsala ta bangaren malamai da matasala ta da carryover wato maimaita wasu daga cikin kwasa-kwasai da ta ke dauka.

Ta ce duk wani matashi dan Najeriya mai tashi a yanzu, bai kamata ya dogara da aikin gwamnati ba, dole su dogara da sana’oin hannu, domin zama masu dogara da kai .

A yanzu dai ta ce, tana aikin hajja, kafin lokacin da Allah zai bata aiki, don ta nuna wa mahaifinta cewar, ko babu aiki, matukar matashi yayi karatu, zai cimma burinsa na rayuwa.