Kwamared Sani Bala wanda aka fi sani da Sani Tela- Lakaci, yayi kira ga Matasa cewa ya kamata su san 'yancin su, haka kuma wajibi ne su san cewa su (matasa) ke da kaso mafi yawa a cikin alummar Najeriya, hakan zai sa su tashi tsaye don tabbatar da cewa matsalar matashi sai matashi ne zai iya magance ta.
Kwamared Sani ya ce 'yan siyasa na amfani da matasa domin su cimma burinsu na cin zabe, da zarar an kammala zabe sai su manta da su.
Matasa a yanzu sun taka duk wata rawa ta cigaba, misali a fannin ilimi, wayewar kai, sanin hanyoyin tafiyar da kasa, a yanzu duk matasa sun san yadda zasu kawo gyara ga Najeriya, sai dai babban abinda ke ci musu tuwo a kwarya ba ya wuce rashin kayan aiki da zasu gudanar da harkar zabe.
Akan haka ne a yanzu matasa ke yunkurin hada kan 'yan uwansu ta hanyar tabbatar da cewa duk wani da yake da sha'awar tsayawa takarar siyasa, sai matasan sun tabbatar da cewa dan takarar yayi wa al'ummarsa aiki kuma ya cancanci kuri'ar su.
Your browser doesn’t support HTML5