Matashi Kamar Danyen Ice Ne Tun Yana Karami Ake Tankwara shi - Aminu Saminu

Aminu Saminu wanda aka fi sani da Varius, Kungiyar A7 support group, ya ce Matasa har yanzu ba’a damawa da su, duba da yadda al’ammuran demokradiya ke tafiya a Najeriya, a da, da farko an fara damawa da matasa daga bisani sai al’amarin ya sauya duk kuwa da cewa an sanya hannu akan kudirin ‘Not too young to run.

Virus ya kuma ce, tun da farko ba’a dora matashi a tsarin da ya dace da shi ba, ko da kuwa gwamnati ta fara wani sabon shiri don inganta matasa sai ta sauya ko ta rasa alkibilar da ta dauka.

Ya bayyana cewa tabas gwamnati mai ci a yanzu ta fito da wasu kudurori amma hakkar ta ba ta cimma ruwa, misali ta fito da harkar noma amma bata maida hankali wajen inganta ilimin matasa a fannin harkar noma ba.

A fannin ayyuka ma hakan ne, ba’a basu horon da ya dace ba don inganta su, duk kuwa da cewa a wasu lokutan su kansu matasa basu maida hankali ba wajen nuna cancantarsu da bukatar son kawo gyara.

A yau, matasa su ne masu shaye-shayen kwayoyi, su ne 'yan sara suka, ana amfani da su wajen bangar siyasa da wasu ayyuka marasa kyau da suke tauye bisarar matasan. Virus ya kara da cewa lallai laifin gwamnati ne, domin matashi tamkar danyen ice ne tun yana karami ake tankwarashi.

ka karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Tunda Farko Ba’a Dora Matashi A Tsarin Da Ya Dace Da Shi Ba 06'13"