Masu Fashin Baki Sunyi Bayani Kan Nasarar Janal Buhari

Kano Celebrations for Buhari

A jiya hukumar zabe ta najeriya INEC, ta sanar da dantakarar Jam’iyyar hamayya ta APC Janar Muhammadu Buhari, a matsayin wanda ya yi galaba a zaben shugaban Najeriya daya wakana ranar Asabar data gabata. Wannan dai shine karon farko da Jam’iyyar hamayya tayi nasarar a zaben shugaba a Najeriya. Dangane da wannan batu ne wakilinmu na Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya tattauna da Dr Sa’idu Ahmad Dukawa masanin kimiyyar siyasa da Farfesa Kamilu Sani Fagge kwararre kan harkokin demokaradiyya da sha'anin diplomasiyya, dukkaninsu malamai a Jami’ar Bayero dake Kano. Saurari tattaunawar