Kare Kai Daga Shiga Damuwar Kishi A Shafin Facebook

A makon da ya gabata ne kamfanin Facebook ya fitar da sanarwar ya fara gwada wata manhaja da zata baiwa mutane damar kare kansu daga shiga damuwar kishi bayan batawa da abokan soyayyarsu.

Manhajar zata baiwa mutum damar rashin ganin duk wani abu da ya shafi tsohuwar budurwa ko tsohon saurayi a kan shafin Facebook, zakuma ta tabbatar da cewa duk abinda tsohuwar budurwa ko saurayi suka kafe a shafin bai karasowa mutum ba.

Wata kwararriya a fannin soyayya mai suna Wendy Walsh tace, “a wannan zamanin shafin sadarwa sun zamanto tabbatatciyar hanya da mutane zasu iya haduwa da tsaffin masoyansu, alokacin da suke tare da sabbin abokan rayuwarsu.

Ta ci gaba da cewa bincike na nunin yadda idan har mutum bai rufe hanya tsakaninsa da tsahuwar zuma ba, ta hanyar sadarwa a yanar gizo, to tabbas zai kasance cikin zafin kishin rabuwa.

Ita dai wannan manhaja da Facebook ke gwado yanzu haka ana iya samunta ne ta wayoyin hannu, kuma anyi gwadon ne ga masu shafukan Facebook a Amurka. Facebook dai zai fitar da manhajar zuwa sauran kasashe nan bada dadewa ba.