Kamfanin InnJoo Zai Fitar Da Sabbin Wayoyinsa A Najeriya

Spain Wireless Show

InnJoo kamfanin kera kayayyakin fasahar nan na Dubai, ya shirya kaddamar da wayoyin zamani har biyu a Jami’ar Lagos gobe Laraba, wanda zai mai da hankali wajen janyo hankalin matasa.

Bukin kaddamar da wannan wayoyi dai zai mayar da hankali wajen neman masalaha ga matsalar wutar lantarki da ake fuskanta a kasar, kamfanin dai zai bayyana wayoyin biyu Halo da Fire Plus, baki ‘dayansu zasu fito ne da babban batiri mai ‘daukar caji da a kalla zai yi kwanaki biyu ba tare da ya kare ba.

An dai shirya za’a gabatar da taron a gobe Laraba 2 ga watan Satumba, inda za’a fara rigistar shiga taron da karfe 3 na yamma. Mawakin nan Adekunle Gold zai yi wasa, sai kuma kungiyar raye-raye ta jami’ar Lagos suma zasu fito su juya domin kayata wannan taro. Sama da mutane dubu 1 ne aka shirya zasu halarci taron, zakuma a rabar da wasu kayyaki da suka hada da wayoyin zamani ga duk wanda suka yi sa’a.

Kamfanin dai yace mutane 200 na farko da suka rigistar wannan taro zasu sami kyautar rigunan da kamfanin ya buga da ba mai irin su, har yanzu dai kamfanin bai fitar da sauran bayanai ba kan wannan wayoyi da zai fitar, Allah dai ya kaimu gobe domin ganewa idanuwanmu.