Jaruma Amina Amal Ta Bayyana Abin Da Ya Hada Ta Da Hadiza Gabon

A shirinmu na nishadi a yau dandalinVOA zai kawo muku hira ne da jaruma Amina Muhammad wacce aka fi sani da Amal dangane da badakalar da ta shiga tsakaninta da jaruma Hadiza Gabon.

Idan masu sauraro na biye da kafafa sadarwa na zamani yana sane da badakalar da ya shiga tsakanin jaruma Hadiza Gabon da Amina Muhammad wacce aka fi sani da Amal har zancen ya kai su ga kotu

A ta bakin jaruma Amal ta ce jaruma Hadiza Gabon na ikrarin cewar sai ta ga bayan Amina Amal, kuma babu kotun da ta isa ta kamata, a cewar ta hakan na nufin ta fi karfin kotu.

Amina Amal ta ce ko da lamarin ya ya du a kafar Instagram ta ce an tursasa ta wajen karyata tare da nuna wa duniya cewar jaruma Amal bata da da’a balle kamun kai.

Ta kara da cewa jaruma Gabon ta nunawa cewa Amal bata da da’a kuma ta na shaye shayen kwaya bayan da ta tursasa ta ta hanya sanya ta a gaba tare da tozartar da ita da cewar idan bata karyata kanta ba lallai zasu yi mata lahani.

Ko da dai cewar dandalin VOA yayi kokarin jin ta baki jaruma Hadiza Gabon hakkarmu bata cimma ruwa, domin mun tura mata da sakon salulula shiru.

Your browser doesn’t support HTML5

Badakala Tsakanin Jaruma Amina Amal Da Hadiza Gabon