Inganta Harshen Hausa Ta Hanyar Salo Da Azancin Zance - Ricqy Ultra

El Yakubu Ismail Ricqy Ultra

Ina kokarin inganta harshen Hausa ta hanyar amfani da salo da azancin zance domin matasan mu masu tasowa inji mawakin gambara El Yakubu Ismail, wanda aka fi sani da Ricqy Ultra.

Ricqy Ultra, ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA a Kanon Dabo. Ricqy, ya ce yana amfani da salon zance kamar su zaurance, Karin Magana da sauransu a cewarsa ta hakanne hanya mafi sauki da za’a iya isar da sako ko kuma koya harshen Hausa.

Ya kara da cewa da farkon fari sukan fuskanci matsalolin rashin gayyatarsu wuraren wassanin domin su baje kolin basirarsu, amma a cewarsa an sami canji domin kuwa a yanzu don jama’a sun fara fuskantarsu tare da manufofinsu.

Daga karshe Ricqy, ya ce yana nusar da matsalolin da ke tattare da nuna kabilanci ko adini ko ma launin fata, tare da nuna ilolin da hakan ke da shi.

Your browser doesn’t support HTML5

Inganta Harshen Hausa Ta Hanyar Salo Da Azancin Zance - Ricqy Ultra