Ina Waka Ne Domin Jan Hankalin Matasa: Aginita Habakkuk

Aginita Habakkuk, wanda aka fi sani da X2dedot mawakin ne na sabon salo na hip-hop wanda aka mai da shi ga salo irin na arewa domin jin dadin masu sauraro, X2dedot yana waka ne akan muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali baya ga fannin nishadantarwa.

Aginita yayi magana akan wakar sa mai suna 'Jini ko ina' waka ce da take fadakar da matasa da ilimantarwa akan su daina barin 'yan siyasa na amfani dasu, wajen bangar siyasa tare da yaudarar su don tada zaune tsaye mussaman ma a lokacin zabe.

Ya kara da cewa lokaci yayi da matasa zasu lura da cewar, su iyayen siyasan nan basa yarda ‘ya'yansu su fito suna bangar siyasa, saboda haka yake kira ga matasa da su lura su kuma tashi su yima kansu fada.

Daga karshe ya ce ya samu alfanu da dama a fannin waka, kuma daga cikin burinsa shine ya daga salonsa na Afropop duk inda ya shiga a dinga cewa ai wannan mawakin Arewa da ya fito da sabon salo ne.

Your browser doesn’t support HTML5

Ina Waka Ne Domin Jan Hankalin Matasa: Aginita Habakkuk 11'03"