Hanya Daya Da Za’a Tallafawa Masata Shine Basu Ilimi - Musadiq Bala

Musadiq Bala matashin dan siyasa wanda ya ce a gaskiya demokradiyyar Najeriya ba ta tafiya da matasa tun daga sama har kasa, domin kuwa babu wani abin ci gaba da za’a zo a ce na ci gaban matasa ne .

Ya ce illa dai gwamnatoci su na durawa matasa kwayoyin domin gudanar da bangar siyasa ta hanyar cika wa iyayen 'yan siyasa wajen cimma muradansu na siyasa.

Ya ce a gwamnatin baya ta dan dama da matasa wajen ba su wasu tallafi na dogaro da kai, duk da dai tallafin baya taka kara ya karya, kamar yadda akan ce da babu gara babu dadi.

Musadiq ya ce hanya daya da za’a tallafi masata shi ne ta hanyar basu ilimi tare da tallafin sana’a mai gwabi, ba wasu kudade na a zo a gani ba, sannan ya kamata matasa su farga su tashi domin kawar da bangar siyasa da kuma samar da damar damawa a matasa a demokradiyyar Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Hanya Daya Da Za’a Tallafawa Masata Shine Basu Ilimi - Musadiq Bala 03'40"