UAE Na Amfani Da Manhajar ToTok Don Leken Asiri

Wata manhaja wadda da ta yi saurin zama sananniya a Hadaddiyar Daular Larabawa don sadarwa tare da abokai da dangi, a zahiri kayan aikin leken asiri ne ke ciki, da gwamnati ke amfani da su don bin diddigin masu amfani da shi, a cewar manema labarai.

Gwamnati ta na amfani da ToTok don bin diddigin hira, da wurare, da hotuna da kuma sauran bayanan duk wadanda suka shigar da manhajar a wayoyinsu, in ji jaridar New York Times, inda suka ambaci jami'an Amurkawan da suka kware wajen tantance bayanan sirri da kuma binciken jaridar.

Hadaddiyar Daular Larabawa ta dade da toshe FaceTime, da WhatsApp da sauran manhajojin hira. Kafofin yada labarai na Daular suna tallata ToTok a matsayin wani zaɓi ga baƙin da ke zaune a ƙasar, don kiran gida da kuma ‘yan uwa da abokan arziki kyauta.

Jaridar The Times na bayyana ToTok a matsayin wata hanya ta bai wa gwamnati damar leken sirri, saboda miliyoyin masu amfani da ita, suna yi don kansu ne suna sanya manhajar a wayoyinsu kuma da saninsu, suke ba da izini da ba da dama ga manhajar.

Kamar sauran manhajoji, ToTok kan buƙaci bayanin wuri wai saboda ta iya samar da ingantattun bayanai game da hasashen yanayi in ji jaridar ta The Times. Hakanan kuma, ta na buƙatar samun dama ga lambobin wayar, da dalilin cewa yana taimakawa masu amfani da ita ne domin hulda da abokai.

Manhajar kuma tana da damar yin amfani da makirofon, kyamarori, kalanda da sauran bayanai.