Facebook Suna Tattaunawa Kan Harajin Mankudan Kudade Na Bilyoyin Daloli

Jaridar Washington Post ta fada a ranar Alhamis cewa wannan itace tara mafi yawa da aka taba dorawa akan duk wani kamfanin fasaha. Jaridar, wacce ta ruwaito kalaman wasu da bata ambaci sunayensu ba, ta ce har yanzu bangarorin biyu ba su amince a kan adadin kudin ba.

Kamfanin Facebook da Hukumar Bunkasa Ciniki ta Tarayyar Amurka watau FTC suna tattaunawa kan “harajin mankudan kudade na bilyoyin daloli” da aka dorawa wa kamafanin sadarwar saboda karya dokokin rufa asirin masu anfani da shi.

Jaridar Washington Post ta fada a ranar Alhamis cewa wannan itace tara mafi yawa da aka taba dorawa akan duk wani kamfanin fasaha. Jaridar, wacce ta ruwaito kalaman wasu da bata ambaci sunayensu ba, ta ce har yanzu bangarorin biyu ba su amince a kan adadin kudin ba.

Kamfanin Facebook ta jima tana fuskantar zarge-zargen taka dokokin bayanan sirri a cikin shekarun da suka wuce. Tun cikin watan Maris Hukumar FTC take binciken abin kunyar da ya shafi kafar ajiye bayanai ta Cambridge Analytica, inda ta tona bayanan siri na mutane kamar miliyan 87 masu anfani da Facebook ba tare da yardarsu ba.

Batun da ake takkadama ko rigima a kansa shine ko Facebook ta saba wa yarjejeniyar shekara 2011 da ta kulla da Kamfanin na FTC, inda tayi alƙawarin kare bayanan sirri na masu amfani da ita. Facebook da FTC sun ki yin sharhi akan wannan al’amari.