DUBAI: Mota Mai Tuka Kanta Zata Fara Sintiri Akan Tituna Don Nemo Masu Laifi

‘Yan sandan kasar Dubai zasu fara amfani da wata karamar mota mai tuka kanta, dake dauke da fasahar yin aiki irin na ‘yan sanda wajen sintiri akan tituna don nemo masu laifi.

Jami’an ‘yan sandan Dubai sun fitar da sanarwar fara amfani da wannan fasaha domin sauya yanayin aikin jami’an tsaro a kasar.

Ita dai wannan mota mai tuka kanta tana ‘dauke da fasahar gane fuskokin jama’a, ta yadda idan ta yi ido biyu da mai laifi zata ganeshi nan take.

Sai dai ba a bayyana cewa ba ko motar zata rika bin motoci da gudu domin kamosu ba. A wajen gwajin fasahar, motar na ‘dauke da kananan jiragen nan masara matuki da ake kira Drones, da za a yi amfani da shi a wajen da motar ke jami’an tsaro ba zasu iya shiga ba.

Jami’an ‘yan sandan Dubai sunce ba sun gabatar da wannan fasaha bane domin maye gurbin aikin mutane da injuna, amma hakan zai taimaka wajen ragewa mutane aiki.

Your browser doesn’t support HTML5

DUBAI: Mota Mai Tuka Kanta Zata Fara Sintiri Akan Tituna Don Nemo Masu Laifi