WASHINGTON D.C —
Tsohon dan wasan gaba na kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa ta Chelsea, Diego Costa, ya bayyana dalilin sa na cewa da ya sani da bai koma kungiya da taka leda ba, ya ce "na yi matukar da na sani".
Coasta ya kwashe kakar wasanni hudu a tsohon kulob din sa kafin ya koma kungiyar Chelsea a shekarar 2014, inda aka yi musayar sa akan zunzurutun kudi Fam Miliyan 32.
Ku Duba Wannan Ma Gareth Ya Amince Da Karin Wa'adin Shekaru HuduCikin shekaru hudu da ya kwashe a kungiyar Stanford Bridge, Costa ya lashe kofunan wasannin Premier League guda biyu.
Karshen wasansa a kungiyar kungiyar Chelsea ya zo ne yayin da ya sami sakon kar ta kwana daga Conte, wanda ya fada masa cewa bashi da makoma mai kyau a kungiyar.