Dalilin da Ya sa Mata ke Tsoron Kadangare

Kadangare

A cikin halittun dake doron kasa Kadangare na daya daga cikin halittun da Mata ke tsoro shin ko menene dalilin haka wakiliyar Dandali Baraka Bashir, ta ji ta bakin wasu mata.

Toh dai Kadangare yawanci idan ya nufo mata, abinda ya sa mata ke guduwa saboda yana shiga cikin jikinsu ko kuma ya shiga wani bangare na mata ka ji ya muntsilinka da sai an wahala kafin a fidda shi dalilin da ya sa mata ke tsoron Kadangare domin babu inda yake nufa sai cikin jikin ka.

Ke kina tsoron Kadangare ya taba razanaki?

A’a saboda yana biyo mata in ya biyu ka cikin jama’a kawai shigewa cikin Hijabi yake yi ya makale sai ana yayewa ko a waje ne kaga dole zaka ji kunya.

Kefa mai ya sa kike tsoron kadangare?

Kawai dai saboda na taba gani ya shiga cikin wandon wata toh shi ya sa nima nake jin tsoron shi.

Toh da ya shige yaya tayi?

Naga damke shi tayi har sai da jini ya fito tama kashe.

Toh baya ga haka ya taba razanaki a cikin jama’a ?

Sosai gaskiya dan in dai na hango shi ko ba wurin na ya nufo ba na kan gudu.

Ke kuma fa?

A’a ina tsoron shi gaskiya kawai akwai tun lokacin da aka taba cewa in an maka asiri dashi in yazo ya shiga jikinka zai ta yawo a jiki ka ne bazai fito ba tun lokacin gaskiya idan na ganshi ko idan yana wuri bana zuwa.

Shi kuwa Dr. Abdullahi Maikano Madaki, masanin halayyar dan Adam dake Jami’ar Bayero dake Kano, cewa yayi, shi Kadangare wata halitta ce wanda kwakwalwar matabata dauke shi abun da zai yi mata adalci ko wani abu mai kyau a jiki ba wanda nada nan idan sun ganshi sakon da kwakwalwa take karba shine wannan abun yakan iya zama illa a garesu kuma sakon gabadaya sai ya shiga duka sassan jiki kwakwalwar ta aika shi wanda ke jawo wa wani lokaci sun firgita sun zubar da abun da suke dauke dashi a lokacin.