Ci Gaba a Masana'antar Kannywood Daga Farfesa Abdallah Uba

Farfesa Abdallah Uba, ya ce ci gaban da aka samu a masana’antar Kannywood na mai hakkar rijiya ne, domin kuwa masu binciken ci gaban fim a wajen yan masana’antar fina-finai tamkar ana muzanta musu ne.

Domin kuwa a cewarsa, basa kallon binciken da malamai na jami’a ko ma wata cibiya ke yi wa harkar a matsayin a wata hanya ta samar da ci gaba, hasali ma sai suke ganin kamar ana nema a bata musu sana’a ce

Ya ce a matsayinsu na manazarta hakkinsu ne su nazarci, su kuma nunawa 'yan masana'antar yadda zasu sauya, domin samun ci gaban da ya dace, ya ce a halin da ake ciki a yanzu, fim labari ne ba kamara ba.

A don haka ne ma yayi yunkurin shigo da wadanda suka yi nisa a harkar damar shigo masana'antar domin a gyara ta, alal misali ya ce ya kawo British council’ domin ta koyawa yan fim yadda ake rubuta labari amma suka jahilci al’amari.

Ya ce kalilan ne suka karbi gayyatar Turawan domin su sami Karin ba ilimin, hasali ma sun fi son su ga suna kyawkyawan yadda ‘yan India suke fina-finansu ta hanyar sanya waka da raye-raye.

Your browser doesn’t support HTML5

Nishadi da farfesa Abdallah