Ana Shirya Fim Akan Almajirai

Almajirai

Matsalar almajirai a arewacin Najeriya, ya kasance matsallar da ya dade yana ciwa yakin tuwo a kwarya. Sabo da haka Moving Image Media na Alhaji Abdulkarim Muhammad Abdulkarim, ke aikin akan wani fim akan matsalolin da suka shafi almajirci da Almajirai.

Alhaji Abdulkarim Muhammad ya ce yakan shirya fina-finai masu nisan zango domin wayar da kan alumma, kan abubuwan dama da zasu ilimatar da jama’a akan zamantakewar yau da gobe.

Ya ce babban kalubalen da ke tattare da kafa kamfanin aikin jarida na kashin kai na tattare da rashin wayewa daga wajen al’umma wajen basu damar baje hajjar sun a ire iren wadannan kamfanoni domin taimakon kai da kai.

Ya bayyana haka ne a yayin zantawa da wakiliyar DandanlinVOA, Baraka Bashir a birnin Kano.

Ya kara da cewa da al’umma dama basu san alfanunsu ba don haka basa basu aiki, da zai inganta harkokinsu, inda ya ke cewa mutane basu san irin muhimmanci bude kamfanin aikin jarida ba, don hakan baya basu damar samun ayyuka daga gare su, har su samu damar daukar wasu mutane aiki a karkashinsu.

Muhammad Abdulkarim ya ce kimanin shekaru 26, kenan da ya bude wannan kamfani bayan dowawarsa daga karatu a kasar wajen, ya ce kamfanin nasu na ayyuka da suka shafi ayyukan jarida, fina-finai da dukkanin dangogin haka.

Ya ce digirisa na farko yayi ne akan abubuwan da suka shafi hada fina-finai da aikin jarida a kasar Amurka , inda daga bisani ya sake yin digirinsa na biyu a aikin jarida a nan gida Nijeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Shirya Fim Akan Almajirai - 4'45"