Ana Iya Nuna Jini, Konewa Ko Wani Ciwo A Jikin Jarumi Duk Da Hoda - Nasir Make-up

Nasir Make-up

Nasir Idris, wanda aka fi sani da Nasir Make-up ya ce tun yana makaranta ya lakanci zane-zane tare da sha’awar gyara mutum ya fito fes hakan ne ya sa, ya tsinci kansa a Kannywood ya karkata ga gyara jarumai su fito fes.

Nasir, ya ce ya shigo harkar fim tun shekarar 1997 a sakamakon yawan kallon fina finan Indiya, da yake yi sai ya lura da yadda ake tsara fim kuma yana burge shi har ya kai ga yana zuwa wuraren da ake shirya fina finai, domin ya kalli yadda suke harka ta fim

Ya ce yana lura da yanayin jarumi kafin ya san irin kalar hodar da ta dace da shi, kafin nan sai an goge fuskar mutum kafin a sanya kalar da zata da ce da jarumi.

Nasir ya kara da cewa ba iya shafa hoda ne abinda yake yi ba ga jarumai a misali wuraren da ake so a nuna jini ko mace ta kone ko wani ciwo duk yana iya yi da hoda ko wasu sinadarai da zai fito kamar na gaske

Ya ce kalubalen da suke fuskanta shine rashin biyan hakki daga masu shirya fim kamar yadda ya dace inda wasu sukan tauye su bayan an kammala masu aiki ko da yake ya ce har yanzu bai kai inda ya ke ba so ya kai ba, daga karshe ya bayyana cewa so yake harkar makeup ta kai shi ga fita kasashen waje.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Iya Nuna Jini, Konewa Ko Wani Ciwo A Jikin Jarumi Duk Da Hoda - Nasir Make-up