Matar Shugaba Mugabe Ta Mika Kanta Ga Jami'an Tsaro Bayan Ta Lakadawa Matashiya Duka Da Wayar Wuta

Shugban kasar Zimbabwe Mr Robert Mugabe, ya isa kasar Afirka ta Kudu, domin ya taimakawa uwargidansa Grace, wadda ta mika kanta ga jami’an tsaron kasar a sakamakon zarginta da lakadawa wata matashiya data kama da ‘ya’yanta a wani dakin Otal duka da wayar wuta.

An zargi matar shugaban kasar ne da laifin lakadawa matashiyar mai suna Gabriella Engels, bayan ta same ta tare da ‘ya’yanta Robrt Jr da Chatunga, suna shan shagali a wani Otal dake birnin Johannesburg, na kasar Afirka ta kudu.

Matashiyar mai shekaru 20 da haihuwa ta nemi a bi mata hakkinta bayan daga hannun matar shugaban kasa Grace Mugabe, wadda ta bata kashi da wayar lantarki, yayin da ta same ta tare da ‘ya’yanta biyu a wani Otal, a birnin Johannesburg.

Matashiyar ta wallafa a shafinta na twitter cewar dattijiya mai shekaru 52, ta bata kashi har ta yi mata rauni a goshi, ta kuma kara da cewa jami’an tsaron matar shugaban sama da goma suna tsaye suna kallo amma basu yi komai ba.