Babban Mufti na kasar Sa’udiyya, wanda shi ne babban malami a cibiyar ta addinin Islama, yayi Allah wadarai da kungiyar Boko Haram a zaman wadda aka kafa domin bakanta sunan Musulunci, ya kuma yi tur da sace dalibai mata su fiye da 200 da kungiyar ta yi.
Sheikh Abdul’aziz al-Sheikh yace wannan kungiyar ta tsageranci, ta kaucewa hanyoyin addini, kuma ya kamata a nuna mata cewa hanyar da ta damka ba ta Musulunci b ace.
Wannan furuci nasa yana zuwa a yayin da manyan shaihunan malamai da shugabannin addini na kasashen Musulmi, wadanda a bay aba su saba fitowa sun a magana kan ‘yan tsagera ba, suka yi caa wajen kusheewa da yin Allah wadarai da kalamun da Abubakar Shekau yayi cewa wai Allah ne yace masa ya sayar da wadannan yara mata da ya sace ga wadanda zasu aure su.