Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

2019 Zasu Karbi Mulki Daga Hannun Jam’iyyar APC


SHUGABANIN JAM'IYYAR APGA
SHUGABANIN JAM'IYYAR APGA

Jami’yyar adawa ta APGA, a Najeriya, ta kamala taron da tayi da shugabanin jami’yyar dake jihohi 36, na kasar

Shugaban jami’iyyar na kasa Dr. Victor Ikechukwu Oye, yace sun tsara wannan taro ne dan kara inganta manufofi da zammar kaucewa duk wani yanayi na rashin bin tsari ko ka’ida.

Yace taron ya basu damar yin waiwaye adon tafiya, ya kara da cewa suna kuma tsara dabarun lashe zaben Gwamna da za’a yi na gaba a jihohin Bayelsa, Kogi da Edo.

Shugaban jami’iyyar ta kasa Dr. Victor Oye,yace yana ji a jikinsa a shekara ta 2019, zasu karbi mulki daga hannun jami’iyyar APC

Masu sharhin kan siyasar Najeriya, na ganin cewa jami’iyyar APGA, ta wata kabila ce ko kuma na wani bangare.

Mr.Labaran Maku shine sabon babban sakataren jami’iyyar na kasa, yace wanna batu ba haka bane yana cewa jami’iyyar APGA, ta masu neman gyaran kasa ne da neman zaman lafiya da kuma habaka tattalin arzikin kasa.

XS
SM
MD
LG