Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zan Kirkiro Shafin Yanar Gizo Da Hausa - Inji Wani Matashi


A taron koya wa daliban tsangaya dabarun aikin jarida da dogaro da kai wanda sashin Hausa na Muryar Amurka da hadin gwiwar jami'ar Bayaro ta Kano suka shirya, wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir ta sami zantawa da wani dalibi matashi mai yunkurin bude shafin labarai na yanar gizo amma da harshen Hausa.

A cewar sa "zan bude shafin amma da harshen Hausa, allal misali ba radio bace, shafi ne na rubutun kawai idan kana so ka nemo labari, sai kawai ka shigar da www, da sauran su, sai kawai kaga labarun sun fito. Duk duniyar da kasan ana amfani da Hausa, zasu iya samin damar shiga wannan shafin."

Wannan zai bada gudummuwar gane duk wani labarin da aka sa da banbance na zamba da kuma na gaskiya.

Hakan zai taimaka mana kwarai wajan gane wanda ya dora labarin da kuma lokacin da aka rubuta shi da ma gane ko wanene ya rubuta shi. domin kasahe da dama inda Hausawa suke basu da irin wannan dama ta samun labarai cikin harshen Hausa. dan haka naga ya dace in aiwatar da wannan dabara.

Matashin yayi karin bayanin cewar ya fuskanci kalubale kamar rashin isassun kudin da zai fara aiwatar da aikin nashi amma a cewar sa, yana sa ran zai sami tallafi daga wurin abokan sa.

XS
SM
MD
LG