Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zamani Ya Sauya Ilimin Ki Rufin Asirin Ki -Inji Malama Safiya Bala


 Malama Safiya Bala Muhammed
Malama Safiya Bala Muhammed

A yau shirin namu na mata yayi baban kamu, domin kuwa mun sami bakuncin mataimakiyar Darakta a ma’aikatar kasa wato Bureau for land management dake jihar Kano wato Malama Safiya Bala Muhamad.

Ta ce ta fuskanci kalubale a yayin da take karatunta na digiri inda ta karanci ilimin taswira da kasa wato Geograpy, a kasancewar ta mace, ilimi ne da a wancan lokaci babu mata da dama sai ‘yan kalilan.

Malama Safiya ta ce duk wani abu da dalibi namiji zai yi a lokacin neman ilimi bashi da banbaci da yadda mata ke yi, kama daga daukar karafa da ake gwajegwaje da zuwa filayen da ake gwajegwajen domin auna yanayin kasa da sauransu duk ba’a dauke wa ‘ya’ya mata.

Hakuma a lokacin babu mata ‘yan arewa sosai amma hakan bai sa ta yi kasa a gwiwa ba, sai ma lamarin ya kara mata kwarin gwiwa.

Daga karshe ta kara da cewa bayan kammala karatun ta sami aiki a ma’aikatar kasa har ta kai mukamin deputy darakta, kuma ta sami dukkanin goyon bayan mai gidanta inda ya mara mata baya har ta kai matsayin da take kai a yanzu.

Malama Safiya ta bukaci ‘ya’ya mata da su jajirce wajen neman nasu na kansu a cewarta zamani ya canza, idan aka ilmantar da diya mace kamar an ilmantar da alumma ce.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:07 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG