Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zamani Ya Saukaka Min Harkokin Kasuwanci - Ramatu Umar


Ramatu Umar, ta ce babban burinta a yanzu dai shine ta bude kasuwar ta a yanar gizo domin tallata hajarta duba da irin cigaban da ake samu, inda ta ke cewa cigaban zamani ya saukaka harkar kasuwanci a yanzu.

Ta ce duk garin da kwastomominta suke ana iya kai masu kaya da zarar sun zabi wanda su ke so ta hanyar kafofin sadarwa da take tallata hajar ta a misali ta whatsapp, da Instagram da ma facebook a cewarta.

Matashiyar ta ce lokaci yayi da mata zasu tashi tsaye domin magance wa kansu kananan bukatu domin taimakawa iyaye a wasu lokutan ma da taimaka wa mai gida mussaman wajen dauke masa bukatun ‘yan uwa.

Haji Ramatu ta kara da cewa babban abinda ke ci ma sana’ar ta tuwo a kwarya dai bai wuce yawan karbar bashi da mutane ke yi su kuma ki biyan bashin akan kare ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:52 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG