Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zakkatul Fitir: Muhimmancinta Da Yadda Ake Fidda Ta


Malam Usaini Uba

Zakatul Fitir zakka ce da ake bada ita bayan an gama azumin watan Ramadana, kafin zuwa sallar Idi.

A cigaba da shirin mu na watan Ramadana yau DandalinVOA ya samu bakoncin Malam Usaini Uba, wani masanin falaki, wato Astronomy a turance, yayi mana tsokaci a kan bayanin Zakatul Fitir da yadda ya kamata a ba da ta.

Zakatul Fitir zakka ce da ake bada ita bayan an gama azumin watan Ramadana, akan bada zakkar ne kafin a tafi sallar Idi, bisa koyarwar manzon rahama.

Ya ce an sunnanta Zakatul Fitir domin tallafawa wadanda basu da karfi samun farin ciki, da walwala a safiyar sallah, bayan an kammala azumin watan Ramadana.

Ya kara da cewa ana so a bada nau'ukan abincin na yanayin al'ummar da zasu bayar da shi, kuma ga wadanda basu da halin samun abincin kaiwa baki, misali a wannan yanki na kasar Hausa an so a bada irin hatsi kamar shinkafa, gero, masara da kuma alkama.

Malam Usaini ya ce gwargwadon awon Zakatul Fitir ana yinsa ne da muddun nabi, wato kwatankwacin kwanon sha na abinci, sannan bayan an auna a kwanon sai a sanya hannu a rairaye tudun awon da aka yi.

A saurari cikakken rahoton wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:46 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG