Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Yiwa APC Kafar Angulu a Jihar Kano


Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso
Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

Yayin da Jam’iyyun siyasa a Najeriya ke daura damarar tunkarar zabukan dake tafe a kasar, wani sabon rikici ya kunno kai a cikin reshen jihar Kano na Jam’iyyar APC biyo bayan aiyyana Dr Hafizu Abubakar a matsayin dan takarar mataimakin gwamnan Kano a karkashin inuwar Jam’iyyar APC.

A farkon wannan wata ne jam’iyyar, ta APC,ta fitar Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin wanda zai yi mata takarar Gwamna a jihar Kano.

Koda yake jam’iyyun ANPP da ACN da CPC, da suka rikide suka zama APC, sun sa ran cewa mataimakin Ganduje, zai fito daga daya daga cikin wadannan jam’iyyu ne, amma kwatsam sai aka sanar da suna Dr.Hafizu Abubakar, wani na hannun damar Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin dan takarar mataimakin Gwamna.

Wannan hukumcin na jam’iyyar ta APC, ya jawon ce-ce-ku-ce a tsakanin magoya bayan Abdulrahaman Kawu Sumaila, daya daga cikin wadanda suka nemi kujerar Gwamnan na Kano, kuma dan asalin jam’iyya ANPP.

Daka dukkan alamu magoya bayan Kawu Sumaila, na neman yin kafar Angulu, a zaben 2015 a jihar Kano.

Kafar Angulu - 3'19"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

XS
SM
MD
LG