Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Fara Tantance 'Yan Wasa 'Yan Kasa Da Shekaru 20


Za'a tantance ‘yan wasan da zasu fafata a gasar cin kofin Alh Aminu Maigari (Live President NFF) na ‘yan kasa da shekaru ashiri U 20.

A shirye shiryen da akeyi na gasar na Alhaji Aminu Maigari (live President NFF) mai taken Alh Aminu Maigari under 20 Youths Football Cup Competition 2016 wanda zai gudana a cikin garin Bauchi
a yau, a filin wasa na tunawa da Sir Abubakar Tafawa Balewa dake cikin garin Bauchi da misalin karfe Goma na safe.
Alh Aminu Maigari ya ce an shirya gasar ne domin hada kan matasa ne a Bauchi da kewaye, da zaman kara dankon zumunci tsakanin matasa, yace tuni dama yana da sha'awar shirya irin wannan gasa tsakanin matasa.

Maigari, ya ce yayin wanan wasan manya manyan manajoji kungiyoyin wasan kwallon kafa zasu hallara domin zakulu yara masu hazaka wadanda za'a daukesu zuwa wasu kungiyoyi da suke buga lig lig don gwaji.


A yanzu haka a fidda kwamitin shirye shiryen wannan gasa mai mutum goma sha daya kar kashi jagorancin Shugaban kwamitin Alh Abdullahi Ibrahim (Askiya), Hon Auwal Baba jada Mataimaki
Alh Yahaya Abdulkareem Sakatare, Danlami a matsayin Mai watsa labarai, Alh Sadiq Yusuf Zaria Mamba
Alh Umar Sa'idu Mamba Alh Nasiru Abdullahi Kobi Mamba, akwai Alh Zailani Ibrahim Alh Bello Mohammed, Mr Paul B Gambar Sauran sun hada da DSP Jostin Takkum Faruq Umar Usman (S Fada).

Wadanan su zasu tafiyar da wanan gasar daga farko har zuwa karshe, Inda ake sa ran cewa ranar Laraba 30/11/2016 za'a fidda jaddawalin rukuni rukuni na wasan a filin wasa na tunawa da Sir Abubakar Tafawa Balewa da misalin karfe goma na safe.
Sannan daga bisani a saka ranan da za'a fara wasan Kungiyoyi talatin da biyu daga cikin kwaryan Bauchi zasu kece raini a tsakaninsu.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG