Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a yi Lattin Kammala Ginin Filin wasan kwallon Rostov


An fara shirye-shiryen gasar kwallon kafa ta duniya wanda za a yi a shekarar 2018 a birnin Rostov na kasar Rasha, amma sai dai za a yi lattin kammala ginin filin wasannin da watannni bakwai bisa ga wa’adin da aka bada.

Hukumar gine-gine ta yankin ta fada a wata sanarwa cewa ranar da ya kamata a gama ginin stadium din, mai kujeru dubu arba’in da biyar, zai wuce watan Maris na shekarar 2017 zuwa watan Disamba.

Hukumar dai bata fadi abinda zai kawo jinkirin ba, amma ta bada wa’adin lokacin da za a gama ginin, yanzu haka dai ma’aikata sun dukufa kan aiki.

A can baya Ministan wasannin kasar Rasha Mr. Vitaly Mutko, wanda kuma ke shugabantar kwamitin shirye-shiryen wasan kwallon kafar, ya fadi cewa yana gani filin wasan garin Rostov na daya daga cikin filayen wasannin Rasha guda sha biyu da zasu yi wahalar ginawa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:54 0:00

XS
SM
MD
LG