Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Ba Da Kyautar Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa Ta Ballon d'Or


A yau litinin 3 ga watan Disamba 2018, za'a ba da kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya ta shekara 2018, Ballon d'Or wadda kungiyar 'yan jaridu marubuta labarin wasanni suke ba da shi duk shekara a kasar Faransa.

Rahotanni sun nuna 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na kasar Spain, su suka fi yawan ‘yan wasa a cikin ‘yan wasa 30 da aka fidda sunanyensu wanda za su kara wajan zaben gwarzon a bana.

Kungiyar na da ‘yan wasa har guda 8 wadanda suka hada da gwarzon 'yan wasan kwallon kafa na Fifa Luka Modric, Varane, Ramos, Marcelo, Isco, Courtois, Bale da kuma Kareem Benzema.

Sauran 'yan takarar su ne Agüero, Alisson, Cavani, Cristiano Ronaldo, De Bruyne, Firmino, Godín, Griezmann, Hazard, Kane, Kanté, Lloris, Mandzukic, Mané, Mbappé, Messi, Neymar, Oblak, Pogba, Rakitic, Salah da kuma Luis Suárez.

Mujallar da ke ba da wannan kyautar ta bayyana sunan tsohon dan wasan kwallon kafa Spurt David Ginola, a matsayin wanda zai jagoranci bikin.

Za'a fara shagulgulan bikin tun daga misalin karfe 4 da rabi na yammaci, inda wasu gidajen talabijin za su fara nunawa har zuwa karfe 8 na yammaci lokacin da za'a bayyana sunan dan wasan da ya samu nasarar lashe kyautar a bana.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG