Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Luka Jovic Zai Buga Wasan Farko a Real Madrid


Luka Jovic

A yau Laraba 12 ga watan Yunin 2019 kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid za ta gabatar da sabon dan wasanta da ta saya, Luka Jovic a gaban dumbin magoya bayanta a filin wasanta na Santiago Bernabeu.

A nan ne dan wasan zai fara sanya rigar Real Madrid, sannan ya shiga fili ya taka ta tamaula, bayan haka kuma idan ya gama zai gana da 'yan jaridu domin bayyana irin yadda ya shirya tunkarar wasanni a kungiyar na tsawon shekara shida.

Jovic ya taho Real Madrid ne daga Eintracht Frankfurt kan yarjejeniyar shekara shida, inda kwantirangtinsa zai kare a karshen kaka zuwa shekara ta 2025.

Ya koma Eintracht ne daga Benfica a matsayin aro a shekarar 2017, inda ya samu nasarar jefa kwallaye 17 a wasa 32 a bangaren Bundesliga da guda 10 da ya zura a wasa 14 da ya buga a Europa Cup.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG