Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar Shekara 12 Mai Sana'ar Reno


'yan mata
'yan mata

A shirinmu na mata na wannan makon, mun waiwayi dabi’ar nan ta yara masu reno ga mata ma’aikata a arewancin Najeriya

Maryam Mohd Idris wata yarinya yar shekara 12, ta ce ta zo ne daga garin Sauna Kawaji a kwaryar birnin Kano domin ta yi sana’ar reno ta kuma tara kudin aurenta

Ta ce da farko mahaifiyar ta na dora mata tallar 'yar tsala daga bisani ta kamu da rashin lafiya wanda ya hana ta cigaba da toya mata 'yar tsala, shine aka kawo ta birnin domin ta yi sana’a a maimakon talla domin tara kudin aurenta da na kashe musu bukatunsu.

Maryamu dai ta ce tana da sha’awar yin karatun boko kafin ayi mata aure

A daya bangaren kuwa uwar dakin Maryamu da ta nemi a sakaya sunanta ta ce a bisa alal lalurati ne suke daukar kananan yara domin basa samun manyan mata .

Ku biyo mu domin jin yadda hirar ta mu ta kasance.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG