Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Wasan Super Falcons Za Su Koma Najeriya A Yau


'Yan wasan Super Falcons na Najeriya

Wannan gasa, na daga cikin shirye-shiryen da ‘yan wasan na Super Falcons ke yi na tunkarar gasar cin kofin duniya ta mata da za a yi a Faransa a wannan shekara.

Kungiyar Super Falcons ta Najeriya, ta kamo hanyar dawowa gida a yau Laraba, bayan da ta kare a mataki na uku a gasar kasashe hudu da aka gudanar a China.

‘Yan wasan na Falcons, sun sha kashi a hannun takwarorin wasansu na China da ci 3-0.

Amma daga baya sun doke kasar Romania da ci 4-1 a filin wasa na Huitang da ke Meizhou.

China wacce ita ta karbi bakuncin gasar, ta lashe kofin bayan da ta lallasa Jamhuriyar Korea.

Wannan gasa, na daga cikin shirye-shiryen da ‘yan wasan na Super Falcons ke yi na tunkarar gasar cin kofin duniya ta mata da za a yi a Faransa a wannan shekara.

  • 16x9 Image

    Mahmud Lalo

    Dan jarida ne da ke aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) a birnin Washington, DC na Amurka. Yana da kwarewa a rassa daban-daban na kafafen yada labarai, kamar wajen hada rahoto a takadar/mujallar jarida, fannin talbijin, rediyo, yanar gizo da kafafen sada zumunta na zamani, inda ya fi mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi shugabanci na gari, ayyukan dogaro da kai, kiwon lafiya da kuma muhalli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG