Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Wasan Super Eagle Sun Tafi Mataki Na Gaba


'Yan Wasan Super Eagle

Tawagar kungiyar kwallon kafa Ta Super Eagles ta Najeriya ta samu nasarar tsallakawa wasan daf na karshe Semi final a turance cikin gasar cin kofin nahiyar kasashen Afirka ta 2019 wanda kasar Masar ta karbi bakunci.

Super Eagle ta samu wannan nasarar ne bayan da ta doke babbar abokiyar hamayyarta kasar Afirka ta Kudu daci 2-1 a wasan na kusa da na kusa da na karshe Quarter Final ranar laraba 10 ga watan Yulin 2019.

Dan wasan Najeriya Chukwueze shi ya fara jefa kwallo a ragar Bafana Bafana acikin minti na 27 da fara wasan.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, Afirka ta kudu ta farke a mintuna na 71 inda dan wasanta Zungu ya jefa kwallon da kai ana 1-1 ana saura minti daya a tashi sai Najeriya ta samu bugun gefe inda dan wasanta Troost Ekong ya jefa kwallo ta biyu

Haka aka tashi yanzu Najeriya zata fafata da Kasar Senegal a wasan daf da karshe na Kofin kasashen Afirka.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG