Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Wasan Najeriya Sun Yi Rashin Nasara A Hannun Senegal


Kungiyar Flying Eagle ta Najeriya sun kara kai wa gaba zuwa wasan daf da kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 20 da ake yi kasar Poland.

Bayan da ta yi rashin nasara a zagayen wasa na 16 da ci 2-1 a hannun Senegal jiya Litinin.

Senegal ta jefa kwallaye biyu a zagayen wasa na farka kafin a tafi hutun rabin lokali, yayın da Flying Eagle ta jefa kwallonta a zagaye na biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Sai dai amma sun ta kai hare hare cikin fushi har zuwa karshen wasan.

'Yan wasan kasar Senegal sun yi ta kokari wajan hana 'yan wasan Najeriya zura kwallo daya da za ta basu dama a sake buga wani karin lokaci na minti 30.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG