Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Wasan Kwallon Kafar Zesco United na Kasar Zambia Sun yi Hatsarin Mota


'Yam wasan Zambia
'Yam wasan Zambia

‘Yan wasan kwallon kafar, Zesco United, na kasar Zambia, su, uku sun samu raunuka, sanadiyar, wani mummunar hatsarin mota, da suka yi akan hanyarsu ta zuwa wajen wasa.

Daya daga cikinsu Nyambe Mulenga, na cikin ayarin ‘yan wasan kasar Zambia, da suka ciwo kofin kwallon kafa, na nahiyar Afirka, na shekaran 2012,

A wata sanarwa, da hukumar kwallon kafa ta kasar ta Zambia, ta fitar, tace mutane hudu ne suka rasa rayukansu, a hatsarin, da suka hada da direban ‘yan wasan na Zesco United na Zambia, da kuma uku a cikin motar da sukayi taho mugama da ita.

Sanarwar ta kara da cewa Mulenga, ya samu tsira da karaya a kafar sa, amma babu wani labari akan sauran ‘yan wasan biyu, na Zesco United, illa dai duk an kaisu asibiti.

'Yan Wasan Zambia - 1'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:54 0:00

XS
SM
MD
LG