Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Pillars Ta Lashe Kofin Aiteo Bayan Doke Tornadoes


Kano Pillars Logo

Kano Pillars ta yi nasarar buga penarti 4 ta zubar da daya, Tornadoes kuwa ta ci uku ta zubar da biyu, inda aka tashi a wasan da ci 4-3.

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi nasarar lashe kofin gasar Federation na Aiteo Cup a wannan shekara bayan da ta doke tawagar ‘yan wasan Niger Tornadoes a bugun penarti.

Sama da shekaru 60 rabon da Pillars ta lashe wannan kofi.

Bangarorin biyu sun fafata ne a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna inda aka kwashe minti 90 har aka yi karin lokaci amma ba a zura kwallo ko daya ba.

Kano Pillars ta yi nasarar buga penarti 4 ta zubar da daya, Tornadoes kuwa ta ci uku ta zubar da biyu, inda aka tashi a wasan da ci 4-3.

A bara, kungiyar ta Kano Pillars da aka fi sani da taken, “Sai Masu Gida” ta sha kaye a hannun Enugu Rangers.

Amma a wannan karon ta sha alwashin huce fushinta a akan 'yan wasan "Ikon Allah" na Tornadoes da suka fito daga jihar Niger.

  • 16x9 Image

    Mahmud Lalo

    Dan jarida ne da ke aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) a birnin Washington, DC na Amurka. Yana da kwarewa a rassa daban-daban na kafafen yada labarai, kamar wajen hada rahoto a takadar/mujallar jarida, fannin talbijin, rediyo, yanar gizo da kafafen sada zumunta na zamani, inda ya fi mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi shugabanci na gari, ayyukan dogaro da kai, kiwon lafiya da kuma muhalli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG