Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Yiwa 'Yar Shekara 9 Fyade


Wata kotu a garin Ilorin ta bada umarnin a daure wani mutun dan makaranta mai suna Oyetunde Ishola, a gidan yari saboda zargin sa da ake yi na yiwa wata yarinya yar shekaru tara fyade.

Da yake jawabi lauya mai gabatar da kara Mr. Ajide Kehinde, yace shi dai wanda ake tuhuma ya yaudari yarinyar ne da ta shiga dakinsa inda yayi mata fyade.

Ya kara da cewa dalilin haka ana tuhumar sa da aikata fyade karkashin sashe na 97 da na 282 na dokar kasa, tuhumar da wanda ake zargi bai amsa ba.

Mai gabatar da karan ya ki amincewa da batun bada beli, saboda a cewar sa doka bata amince da abada beli ga wanda ake zargi da aikata fyade ba.

Mai sharia Foluke Olokoyo, ta amince da batun na mai gabatar da kara ta kuma umarci a wuce da shi gidan yari har zuwa 8, ga wannan watan na Oktoba.

XS
SM
MD
LG