Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yayi Mata Alluran Barci Domin Yayi Mata Fyade


An gurfanar da wani ma’aikacin jinya,ko kuma Nas, Olugbenga Isaac, mai shekaru ashirin da bakwai, a kotu, bisa zargin cewa ya yiwa wata yarinya ‘yar shekaru goma sha tara fyade bayan yayi mata alluran barci.

Mai gabatar da kara sufeton ‘yan Sanda, Clifford Ogu, ya gayawa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne ranar 15, ga watan Satumban wannan shekarar a unguwar Onipanu, a birnin Legas.

Ita dai wannan yarinya tana fama da ciwon kai ne sai ta gayawa Olugbenga, kasancewarsa ma’aikacin jinya a maimakon ya yimata maganin ciwon kai sai ya yimata alluran barci kuma yayi amfani da wannan damar domin yayi mata fyade.

Laifin da ake zargin Olugbenga, da aikatawa ya sabawa sashe na 258,na kundin laifuffukan jihar Legas na shekarar 2011.

Mai shara’a, Mrs.T. Akanni, ta bada belin wanda aka zargin akan kudi Naira dubu dari biyu, kuma an dage shara’ar zuwa 30, ga watan Nuwamba na wannan shekarar.

XS
SM
MD
LG