Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Tabbata Za'ayi Zabe a Arewa Maso Gabashin Najeriya


Ma'aikatan Zabe
Ma'aikatan Zabe

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, yace don neman mulki abokan hamayya za suyi amfani da kowace kafa na tsoratarwa, kage da amfani da kafufin watsa labarai ‘yan gaza gani da sauransu.

Yayi wannan furuci ne a lokacin da yake wa magoya bayansa jawabi a wurin kamfe, yana mai cewa abune mai kara karfin gwiwa yanda harkokin tsaro, suka dan inganta, kuma idan Allah, ya yarda za’a yi zabe a duk jihohin Najeriya.

Suma a nasu bangare magoya bayan canji zuwa Gwamnatin adawa, sanata Danjuma Goje, na ganin jamiyya mai mulki, ke da hanyoyin razanarwa ko takurawa adawa.

‘Yan takaran zabin jam’iyyun adawa ma na ganin tabarmarsu na da fadin daukar wadanda suka kasa samun adalcin manyan jam’iyyu, a nasu ra’ayin kuma suna hangi nasara, inji Barrister, Kabiru Dodo dan takarar Gwamna na jami’yyar PDM a jihar Taraba, a wata ganawa da suka yi da wakilin muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikay, a Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

XS
SM
MD
LG