Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Samu Nasarar Lashe Manyan Kofuna Daban Daban A Barcelona


Barcelona's Adriano Correia, Ivan Rakitic and Andres Iniesta, from left, celebrate with the trophy after winning 3-1 the Champions League final soccer match between Juventus Turin and FC Barcelona at the Olympic stadium in Berlin Saturday, June 6, 2015. (
Barcelona's Adriano Correia, Ivan Rakitic and Andres Iniesta, from left, celebrate with the trophy after winning 3-1 the Champions League final soccer match between Juventus Turin and FC Barcelona at the Olympic stadium in Berlin Saturday, June 6, 2015. (

Shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Spain mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, mai suna , ya ce babban burinsa a rayuwa a harka tamola shine ya karkare harkar kwallon a kungiyarsa ta Barcelona.Andres Iniesta
Iniesta ya ce ya dade da wannan buri a zuciyarsa, shida Iniesta ya fara murza tamola ne a kungiyar kwallon kafa mai suna La Masia Youth Academy a lokacin yana dan shekara 12 da haihuwa inda daga bisani ya koma kungiyar kwallon kafa ta Barcelona a watan Oktoba na 2002, kemanin shekaru goma sha takwas kenan da suka wuce.
Andres Iniesta ya ce yana jin dadi zamanza a Barcelona, inda ya samu nasarar lashe wasu manyan kofuna daban daban har sau takwas wanda ya hada da Copa del Rey na kasar Spain, Sau hudu sai kofin zakarun nahiyar Turai (UCL) shima sau hudu da kuma Club World Cup duka a kungiyar ta Barcelona.
A yanzu haka dai Iniesta yana da shekaru talatin da biyu da haihuwa a duniya, kuma kwanteraginsa zai kare a Barcelona, a shekara ta 2018 sai dai mahukunta kungiyar na sha'awar son sake tsawaita zamarsa a kungiyar ta Barcelona.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00

XS
SM
MD
LG