Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kwashe Shekaru 29 a Gidan Yari Batare da Laifi ba


Gidan Yari
Gidan Yari

Wani mutun dan shekaru hamsin da takwas da haihuwa da aka kulle a gidan sarka a Amurka Allah yayi masa gyadar dogo ya samu fitar bayan da ya kwashe tsawon shekaru ashirin da tara a kulle.

Michael McAlister, dai kulle shi dangane da zargi sa da ake yi a wancan lokacin na kokarin aikata fyde, a shekarar 1986, a wani dakin wanki a virginia, kusa da birnin Washington.

Daga baya sai aka kama wani Norman Bruce wanda ake tuhumasa da aikata laifin mai na saba da cin zarafin mata bayan da aka gudanar da bincike aka kuma kama shi da aikata laifin daga bisani sai ya ambatawa mahukumta cewa a shekarar 1986, shine ya aikata wannan laifin a dakin wanki, dalilin da yasa Gwamnan jihar Virginia yayiwa Michael McAlister ahuwa.

Tuni McAlister, ya sadu da mahaifiyar sa da kuma 'yar uwansa suka nufi gida.

XS
SM
MD
LG