Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Ga Zoben Sa Bayan Shekaru Arba'in Da Fadawa Cikin Ruwa


Wani mutum a Birnin New York na kasar Amurka ya yarsda zoben sa kuma bayan shekaru arbain ya sake tsintar kayan sa kuma ya tabbatar da lallai wannan zoben sa ne da ya fadi.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, mutumin mai suna Jim ya auri wata mata mai suna Jane a shekarar 1960, kuma sun bukukuwa da dama har ma sun je yawon shakatawa a wani rafi da aka kebe domojn masu zuwa yawon shakatawa wanda a gefen rafin ne zoben da amaryar sa ta bashi ya subule ya fada cikin ruwan.

A kwai wata mata dake zuwa wannan wurin shakatawar a kusan ko wane karshen watan Agust wadda ta yi sa’a ta hangi wani abu mai kamar zinariya a cikin ruwa dai dai inda zoben Mr Jim ya kufce, kawai sai ta shiga ta sa hannu ta dauko sai kawai taga zoben zinare ne kuma yana dauke da sunan mai zoben tare da kwanan watan da aka daura masu aure wato 2-6-1960.

Wannan mata dai ta hanunta zoben ga jama’ar da ke zama a kusa da wannan rafi inda su kuma suka fara cigiya har Allah ya sa maganar ta akai ga kunnen Mr Jim.

Mutumin ya kasance mai matukar farin cikin sake samun zoben sa da ya rabu da shi sama da shekaru arba’in, jama’a da dama sun yi mamakin irin wannan lamari kuma abin al’ajabi.

Abin tambaya anan shine, idan kai ne ko kece kika tsinci zoben zinariya da suna da kwanan wata rubuce a jikin sa, za kayi cigiya?

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG