Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wikki Tourist Ta Fara Da Kafar Dama


Mustapha Wikki Tourist
Mustapha Wikki Tourist

A wasannin da ake fafatawa a can jihar Enugu na tarayyan Najeriya tsakanin manyan manyan Kungiyoyin kwallon kafa na kasar guda hudu watau (Top 4)wadanda suka lashe gasar firimiyan da ta gabata.
kungiyoyin sune Enugu Rangers da ta lashe firimiya 2016 sai Rivers United da ta zamo na biyu Sauran sune Wikki Tourist na garin Bauchi da tayi na uku a gasar ta firimiya lig tare da Ifeanyi Ubah da ta zo na hudu.
A jiya laraba a wasannin da aka fara don neman zakara a tsakaninsu kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist ta samu nasaran doke takwaranta kungiyar Ifeanyi Ubah da ci 2,da1, Kungiyar Ifeanyi Ubah ce ta fara jefa kwallon a ragar Wikki bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Daga bisani Wikki Tourist ta samu nasarar farke kwallonta ta kafan dan wasanta mai suna Shaman inda daga karshe kungiyar ta wikki ta sake samun dama jefa kwallonta na biyu ta kan dan wasanta mai suna Abdullahi a lokacin Saura mintuna biyu na karin lokaci a karkare wasan.
Ita kuwa mai masaukin baki Enugu Rangers ta lallasa Rivers United ne da kwallaye 2-0, Inda a yanzu haka Wikki zata fafata da Enugu Rangers a wasan gaba kaftin din Wikki Mustapha Ibrahim ya baiyana ma Dandalinvoa cewa suna da kwarin guiwa wajan lashe wannan kofi kar kashin jagurancin sabon kocinsu Baba Ganaru Wanda ya kama aiki da kungiyar a bana bayan tafiyar tsohon kocinta Maikaba.
Kungiyar dai ta Wikki ana ganin ta fara da kafar dama domin a satin da ya wuce ne ta lashe kofin Shehu Dikko pree season 2016 acan Kaduna.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG