Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wayar Salula ta Galaxy S5


Wayar salula ta Kamfanin Samsung wato Galaxy S5 itace dai waya mafi fasaha da kamfanin ya taba yi da fitar da ita kasuwa, amma kamfanin ya fitar da wani rahoto cewa wayar ta Galaxy S5 bata samun kasuwar daya kamata, kamfanin dai ya bayyana cewa wayar daya fitar ta baya wato Galaxy S4 tafi shiga kasuwa fiye da sabuwar wayar Galaxy S5.

An dai fitar da wannan wayar kasuwa a watan Afirilun daya wuce, an fitar da wayar ne domin kashe wa iphone 6 kasuwa.

Kamfanin dai ya sayar da kan wayar har miliyan 12, cikin watanni uku da fitar da ita kasuwa, idan kuma aka duba a daya bangaren kamfanin ya sayar da galaxy S4 har miliyan 16. Samsung dai bai bayyana ainihin cinikin da yayi ba, amma kamfanin na fitar da rahotan faduwar riba kusan saba’in da hudu cikin dari na ribar dayake samu a baya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:01 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG