Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Kasuwa sun Fada Cikin Halin Rudani da Rashin Tabbas


Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja
Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja

A yanzu haka dai wasu kananan ‘yan kasuwa sun fada cikin halin rudani da rashin tabbas game da makomar kudadesu, da sukayi ajiya a wani karamin Bankin bada rance ga kananan ‘yan kasuwa, a jihar Neja.

‘Yan kasuwar dai sun ce yanzu kimanin watani shida kennan suna son fidda kudadensu daga Bankin, mai suna “Tattali Micro Finance” dake Makera a karamar hukumar Mashegu, amma hakan bata samuba domin kuwa basu ganin kowa a Bankin, al-amarin da suka ce ya rikitar da hankalinsu.

Wakilin muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari, yayi kokarin tuntubar Shugaban hukumar gudanarwar Bakin Haruna Dan Gajere, da kuma jami’an Gwamnatin jihar Neja akan batun amma hakan ya ci tura.

Sama da fadi da kudade -2'58"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

XS
SM
MD
LG