Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Matasa Dalibai Sun Kirkiro Fasahar Kashe Wuta Da Sauti Zalla


Wani dan kwanakwana na kokarin kashe wuta
Wani dan kwanakwana na kokarin kashe wuta

A cigaba da kirkiro fasahohin ban al’ajibi da matasa ke yi a fadin duniya, wasu daliban fanni injiniya na Jami’ar George Mason da ke nan Amurka su biyu, sun kirkiro wata fasahar kashe wuta da sauti zalla.

Wannan fasahar ta kunshi auna wutar da lasfikar na’urar sautin, ta yadda karar za ta tinkari wutar ta rikita wutar, ta kasa ci, ta mutu nan da nan.

Tuni daliban, wato Seth Robertson da Viet Tran su ka gwada ma jama’a ingancin wannan fasahar ta su, ta wajen kunna wuta mai harshe sosai, su ka kuma kashe wutar cikin ‘yan dakikoki da wata ‘yar kara da ke fitowa daga lasfikar na’urar.

Matasa Robertson da Tran, na ganin nan gaba fasaharsu za ta maye gurbin sinadarin kashe wuta mai guba da kuma sa wuri ya cabalbale.

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:55 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG