Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wanne Kura Kurai Ya Kamata Maza Su Gujewa Na Bangaren Saduwar Aure?


Daurin Aure a Kano, Disamba 19, 2013
Daurin Aure a Kano, Disamba 19, 2013

Saduwa ta ma’aurata na da sharuda da ka’idoji wadanda mafi yawancin lokuta ma’aurata ba su damu da bin wadannan sharuda da ka’idoji ba, wanda baki daya bangaren maza da mata kowanne na da kuskuren da yake yi akan wannan. Kan haka ne shirin Yau Da Gobe ya duba bangaren maza domin gano kowanne kura kurai ya kamata su gujewa.

A kwai sharuda da ka’idoji na saduwar aure da yakamata ace ma’aurata na bi, amma mafi yawancin lokuta ma’aurata basu damu da bin su ba. Shirin Yau Da Gobe ya gayyato masanin ilimin zamantakewa da halayyr dan Adam, Mallam Muhammad Hadi Musa na kwalejin share fagen shiga jami’a a jihar Kano ta Najeriya.

Mallam Muhammad, ya fito balo-balo kuma dalla dalla akan ilimin jima’I kamar yadda ya kamata a koyar kafin a yi aure. Inda ya fitar da wasu sharuda da yakamata maza su bi wajen neman saduwa da matansu, na farko shine mutum ya duba lokacin da ya kamata, domin bai kamata ba ace mutum ya afkawa matarsa lokacin da take barci ko tana yin wasu ayyuka ko tana tare da iyayenta ko kawayenta da dai sauransu.

Sharadi na gaba shine tabbatar da guri mai kyau, dana da kyau namiji ya dauba yanayin gurin da zai sadu da matarsa cikin kwanciyar hankali, ta hanyar tabbatar da gurin bai fiya sanye ko zabe mai tsanani ba, kuma inda mace ba zatayi fargabar ko wani na iya shigowa ba alokacin da suke kwance.

Yana da matukar muhimmanci ace namiji ya kula da tsaftar jikinsa, wannan kuwa ya hada da wanke baki domin tabbatar da baya wari, da lura da jiki domin wasu lokuta mutum kan dawo daga kasuwa ya sha rana hammata na ta wari ba tare yin wanka ba mutum yace zai sadu da matarsa, hakan na iya tayarwa da matar hankali da rashin nutsuwa.

Saurari Mallam Hadi Musa don jin cikakken bayani.

XS
SM
MD
LG