Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Yaro Mai Shekaru 10 Ya Lashe Kyautar Dala Dubu Goma Daga Facebook


Kamfanin Facebook ya baiwa wani yaro dan shekara goma da haihuwa kyautar Dala Dubu 10 kwatankwacin Naira Miliya Biyu, bayan da yaron ya gano wata budaddiyar kofa a manhajar Instagram.

Yaron mai suna Jani, wanda ba a bayyana cikakken sunansa ba saboda tsaro, shine karamin yaro da ya taba samun shiga gasar masu kutse da kamfanoni da gwamnatoci ke amfani da su wajen nemo duk wata gurbatacciyar kofa a shafikansu na yanar gizo.

A lokacin da Jani ke magana da wani gidan jaridar Findland, yace yayi kokarin ganin ko zai iya yiwa Instagram kutse, sai gashi yayi. Kamfanin Facebook dai yace ya gyara wannan hanya da Jani ya samo tun watan Fabarairu, kuma ya baiwa yaron tukwicinsa a wata Maris.

Duk da yake dai Jani yayi kankanta da ya bude shafin Facebook or Instagram, amma yace ya koyi yanda akeyi wannan kutse ta hanyar kallon hotan bidiyo a dandalin Youtube, inda ya samo hanyar da zai goge bayanai da mutane suka rubuta a shafukansu na Instagram.

Daga karshe yaron yace yana tunanin yin karatunsa kan harkar tsaron bayanai a yanar gizo, amma shirinsa na yanzu shine ya sayi sabon keke da kwallon kafa da kudin da ya samu.

XS
SM
MD
LG